26 Agusta 2022 - 19:56
Japan : Shugaban ‘Yan Sanda, Ya Aje Aiki, Saboda Kisan Shinzo Abe

Shugaban ‘yan sanda Japon, Itaru Nakamura, ya mika takardar murabus dinsa bayan gano gazawa wajen tsare tsohon firaministan kasar Shinzo Abe, wanda yam utu sakamakon harbin bindiga a ranar 8 ga watan Yuli da ya gabata.

Shugaban ‘yan sanda ya ce ya yi hakan ne domin baiwa sashen tsaro yin wani sabon shiri.

Ya ce kisan Shinzo Abe, wani lamari ne da ya kamata a ce an kauce wa faruwarsa, amma aka samu nakasu.

Ya kuma ce ba’a tabbatar da tsaro ba yadda ya kamata a dandalin da tsohon firaministan zai yi jawabi, sannan makashinsa ya wuce salin alin dauke da jaka da bindiga kirar gargajiya ba tare da an caje shi ba.

Haka kuma masu gadinsa basu fahimci cewa ba karar farko da akaji bindiga ce, wanda da sun yi hakan da zasu iya bindige maharin kafin harbi na biyu.

Ana dai aza ayar tambaya kan mi yasa murabus din shugaban ‘yan sanda ta zo a yanzu, a daidai lokacin da kasar ke shirin guduanar da jana’izar ag tsohon fira ministan a watan Satumba, wanda ake sa ran manyan jami’an kasashen duniya zasu halarci bikin ciki har da mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris.

342/